25 Kada ku fita zuwa gona,Kada kuma ku yi yawo a kanhanya,Gama abokin gāba yana da takobi,Razana a kowane sashi.”
26 “Ya mutanena, ku sa tufafin makoki,Ku yi birgima cikin toka,Ku yi makoki mai zafi irin wandaakan yi wa ɗa tilo,Gama mai hallakarwa zai auko mananan da nan.”
27 Ubangiji ya ce wa Irmiya,“Na maishe ka mai aunawa da maijarraba mutanenaDomin ka sani, ka aunaal'amuransu,
28 Su duka masu taurinkai ne, 'yantawaye,Suna yawo suna baza jita-jita.Su tagulla ne da baƙin ƙarfe,Dukansu lalatattu ne.
29 Ana zuga da ƙarfi,Dalma ta ƙone,Tacewar aikin banza ne,Gama ba a fitar da mugaye ba.
30 Ana ce da su ƙwan maƙerar azurfane,Gama ni na ƙi su.”