11 “Ni Ubangiji na ce, zan mai daUrushalima tsibin kufai,Wurin zaman diloli,Zan kuma mai da biranen Yahuzakufai, inda ba kowa.”
12 Wa yake da isasshiyar hikimar da zai fahimci wannan? Wa Ubangiji ya faɗa masa don ya sanar? Me ya sa ƙasar ta lalace ta zama kufai, har ba wanda yake iya ratsa ta, kamar hamada?
13 Sai Ubangiji ya ce, “Saboda sun bar dokata wadda na sa a gabansu, ba su yi biyayya da maganata ko su yi aiki da ita ba.
14 Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba'al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu.
15 Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi.
16 Zan watsa su cikin sauran al'umma waɗanda su da kakanninsu ba su san su ba, zan sa takobi ya bi su don in hallaka su.
17 “Haka ni Ubangiji Mai Runduna nace,Ku yi tunani, ku kirawo mata masumakoki su zo,Ku aika wa gwanaye fa.”