11 Ubangiji ya miƙa dantsensa a kan tekun, ya hamɓarar da mulkoki. Ya umarta a lalatar da manyan biranen ciniki na Taya.
12 Birnin Sidon, farin cikinki ya ƙare. Ana zaluntar jama'arki, ko da za su tsere zuwa Kubrus duk da haka ba za su zauna lafiya ba.
13 (Mutanen Babila ne, ba na Assuriya ba, waɗanda suka bar namomin jeji su murƙushe Taya. Mutanen Babila ne suka gina hasumiya, suka ragargaza kagarar Taya suka bar birnin kango.)
14 Ku yi hargowar baƙin ciki ku matuƙan jiragen teku! An hallaka birnin da kuke dogara gare shi.
15 Lokaci yana zuwa da za a manta da Taya har shekara saba'in, gwargwadon kwanakin sarki. Bayan waɗannan shekaru kuma, Taya za ta yi waƙa irin ta karuwa, cewa
16 “Ɗauki garayarki, kewaya cikin gari,Ayya, an manta da karuwa!Yi kiɗa, sāke raira waƙoƙinki,Don ki komo da masoyanki.”
17 Bayan shekara saba'in ɗin, Ubangiji zai bar Taya ta koma a kan cinikinta na dā, za ta ba da kanta ijara ga dukan mulkokin duniya.