18 Sa'an nan zai fita ya tafi wurin bagade wanda yake gaban Ubangiji don ya yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimin da na bunsurun, ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye.
19 Zai kuma yayyafa jinin da yatsansa har sau bakwai a kan bagaden, ya tsabtace shi, ya tsarkake shi daga ƙazantar jama'ar Isra'ila.
20 A sa'ad da ya gama yin kafara don Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden, sai ya miƙa bunsuru ɗin mai rai.
21 Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra'ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi.
22 Bunsurun zai ɗauki muguntarsu duka a kansa zuwa jeji. Mutumin kuwa zai sake shi can a jeji.
23 Sa'an nan Haruna zai shiga alfarwa ta sujada, ya tuɓe tufafinsa na lilin waɗanda ya sa sa'ad da ya shiga Wuri Mafi Tsarki, ya ajiye su a nan.
24 Zai kuma yi wanka da ruwa a wuri mai tsarki, sa'an nan ya sa tufafinsa, ya je, ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadaya ta ƙonawa don jama'a, domin ya yi kafara don kansa da jama'a.