12 Musa kuwa ya aika a kirawo Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, amma suka ce, “Ba za mu zo ba!
13 Kana jin ƙaramin abu ne da ka fitar da mu daga cikin ƙasar mai yalwar abinci, don ka kashe mu a jeji? So kake kuma ka mai da kanka sarki a bisanmu?
14 Banda wannan kuma, ga shi, ba ka kai mu zuwa cikin ƙasa mai yalwar abinci ba, ba ka ba mu gonaki da gonakin inabi domin mu gāda ba, yanzu kuwa kana so ka ruɗe mu, to, ba za mu zo ba sam!”
15 Musa kuwa ya husata ƙawarai da gaske, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace ko jakinsu ba, ban kuwa cuce su ba.”
16 Musa ya ce wa Kora, “Kai da ƙungiyarka duka ku hallara a gaban Ubangiji gobe, da kai, da su, da Haruna.
17 Sa'an nan kowane ɗayanku ya ɗauki farantinsa na ƙona turare, ya zuba turaren wuta a ciki, ya kawo a gaban Ubangiji, wato farantan ƙona turare guda ɗari biyu da hamsin ke nan. Kai kuma da Haruna kowannenku ya kawo nasa faranti.”
18 Sai kowannensu ya ɗauki farantinsa, ya zuba wuta a ciki, sa'an nan ya zuba turaren wuta, suka tsaitsaya a bakin ƙofar alfarwa ta sujada tare da Musa da Haruna.