21 Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.
22 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
23 A rana ta huɗu ta idin za a miƙa bijimai goma, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.
24 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.
25 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
26 A rana ta biyar ta idin za a miƙa bijimai tara, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.
27 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.