4 Sai ku aiki mutum dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila zuwa wurin yaƙi.”
5 Aka samo mutum dubu goma sha biyu (12,000) shiryayyu don yaƙi, daga cikin dubban Isra'ilawa, mutum dubu ɗaya daga kowace kabila.
6 Musa ya aike su zuwa yaƙi tare da Finehas, ɗan Ele'azara firist, da akwatin alkawari, da ƙahonin kiran yaƙi a hannun Finehas.
7 Suka yi yaƙi da Madayanawa suka kashe musu kowane namiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
8 Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal'amu ɗan Beyor.
9 Isra'ilawa suka kwashi mata da yaran Madayanawa bayi. Suka washe shanunsu, da tumakinsu da dukan dukiyarsu ganima.
10 Suka kuma ƙone dukan biranen zamansu da dukan san saninsu da wuta.