6 Musa ya aike su zuwa yaƙi tare da Finehas, ɗan Ele'azara firist, da akwatin alkawari, da ƙahonin kiran yaƙi a hannun Finehas.
7 Suka yi yaƙi da Madayanawa suka kashe musu kowane namiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
8 Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal'amu ɗan Beyor.
9 Isra'ilawa suka kwashi mata da yaran Madayanawa bayi. Suka washe shanunsu, da tumakinsu da dukan dukiyarsu ganima.
10 Suka kuma ƙone dukan biranen zamansu da dukan san saninsu da wuta.
11 Da mutum da dabba sun kwashe su ganima.
12 Suka kawo bayin da ganimar a wurin Musa, da Ele'azara firist, da taron jama'ar Isra'ila a zango a filayen Mowab a Kogin Urdun daura da Yariko.