5 “Ba su koma ƙasar Masar ba,Amma Assuriya za ta zama sarkinsuGama sun ƙi yarda su koma wurina.
6 Takobi zai ragargaje biranensu,Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu,Zai cinye su domin muguwar shawararsu.
7 Mutanena sun himmantu su rabu da ni,Ko da yake an kira su ga Ubangiji,Ba wanda ya girmama shi.
8 “Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu?Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila?Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma?Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim?Zuciyata tana motsawa a cikina,Juyayina ya huru.
9 Ba zan aikata fushina mai zafi ba,Ba zan ƙara hallaka Ifraimu ba,Gama ni Allah ne, ba mutum ba,Maitsarki wanda yake tsakiyarku,Ba zan zo wurinku da hasala ba.
10 “Za su bi Ubangiji,Zai yi ruri kamar zaki, hakika zai yi ruri'Ya'yansa za su zo da rawar jiki da yamma.
11 Da sauri za su zo kamar tsuntsaye daga Masar,Kamar kurciyoyi daga ƙasar Assuriya,Zan komar da su gidajensu, ni Ubangiji na faɗa.”