12 Wane mu mu daidaita kanmu, ko mu gwada kanmu da waɗansu masu yabon kansu! Ashe, waɗannan mutane masu auna kansu da juna, suna kuma neman bambanci a tsakaninsu da juna, ba su da basira.
13 Amma dai ba za mu yi alfarma fiye da yadda ya kamata ba, sai dai mu tsaya a kan iyakar da Allah ya yanke mana, wadda ta game har da ku.
14 Ai, ba mu wuce gona da iri ba, kamar ba a hannunmu kuke ba, domin mu ne muka fara shan nisa, muka je a gare ku da bisharar Almasihu.
15 Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba ta kuma shafi aikin waɗansu ba. Amma muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku ya riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske,
16 har ma mu samu mu yi bishara a ƙasashen da suke a gaba da ku, ba tare da wata fahariya da aikin da wani ya riga ya yi a fagensa ba.
17 Amma, “Duk mai yin fahariya, ya yi fahariya da Ubangiji.”
18 Ai, ba mai yabon kansa ake yarda da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.