2 Nahash Ba'ammone kuwa ya ce, “Zan ƙulla amana da ku a kan wannan sharaɗi, wato in ƙwaƙule idanunku na dama don ku zama abin raini ga Isra'ilawa.”
3 Dattawan Yabesh kuwa suka ce masa, “Ka ba mu zarafi kwana bakwai domin mu aika da manzanni a dukan ƙasar Isra'ila, idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, to, sai mu ba da kanmu gare ku.”
4 Da manzannin suka zo Gibeya inda Saul yake, suka ba mutane labarin abin da ya faru. Sai jama'a duka suka yi kuka.
5 Saul kuwa yana dawowa daga gona ke nan, tare da shanunsa na huɗa. Sai ya ce, “Me ya sami jama'a suke kuka haka?” Suka faɗa masa labarin mutanen Yabesh.
6 Da Saul ya ji, sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.
7 Ya kwance shanun, ya yanka gunduwa gunduwa, ya aika da su ko'ina a ƙasar Isra'ila ta hannun manzanni, yana cewa, “Duk wanda bai fito ya bi Saul da Sama'ila ba, to, haka za a yi da shanun nomansa!”Jama'a suka ji tsoron abin da Ubangiji zai yi, suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.
8 Sa'ad da Saul ya tara mutane a Bezek, aka sami mutum dubu ɗari uku (300,000) daga Isra'ila, dubu talatin (30,000) kuma daga Yahuza.