1 Sama'ila ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Ga shi, na kasa kunne gare ku, na kuwa yi muku abin da kuka ce mini, na naɗa muku sarki.
2 Yanzu ga sarki a gabanku, 'ya'yana maza kuma suna tare da ku. Ni na tsufa, na yi furfura, amma na yi ta kai da kawowa a cikinku tun ina yaro har zuwa yau.
3 To, ga ni nan, ku shaida a kaina a gaban Ubangiji da gaban wanda Ubangiji ya naɗa sarki. Takarkari ko jakin wa na ƙwace? Wa kuma na zalunta, ko na wulakanta? A wurin wa na karɓi hanci don in danne gaskiya? Sai ku shaida, ni kuwa zan mayar masa.”
4 Jama'a suka amsa, suka ce, “Ba ka zalunci kowa ba, ba ka wulakanta kowa ba, ba ka kuma yi wa kowa ƙwace ba.”
5 Sa'an nan ya ce musu, “Ubangiji shi ne shaida, wanda kuma ya naɗa, shi ma shaida ne a yau, cewa ba ku iske ni da laifin kome ba.”Jama'ar suka ce, “Ubangiji ne shaida.”
6 Sama'ila kuma ya ce wa jama'a, “Ubangiji ne ya sa Musa da Haruna su fito da kakanninku daga ƙasar Masar.
7 Yanzu fa ku tsaya shiru don in yi muku magana a kan ayyuka masu adalci na Ubangiji waɗanda ya aikata dominku da kakanninku.