20 Sama'ila kuwa ya ce musu, “Kada ku razana, gama kun riga kun aikata wannan mugunta, duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta masa da zuciya ɗaya.
21 Kada kuma ku ratse ku bi abubuwa marasa amfani da ba za su amfane ku, ko su cece ku ba, gama ba su da wani amfani.
22 Gama Ubangiji ya yi ƙaƙƙarfan alkawari, ba zai yashe ku ba, gama ya ɗauri aniya ya maishe ku jama'arsa.
23 Amma ni kaina, Allah ya sawwaƙa in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin fasa yin addu'a ga Ubangiji dominku. Zan riƙa koya muku kyawawan abubuwan da suke daidai.
24 Ku dai ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aminci, da zuciya ɗaya. Ku tuna da manyan al'amuran da ya yi muku.
25 Amma idan kuka ci gaba da aikata mugunta, za a shafe ku, ku da sarkinku.”