1 Sai Saul ya yi magana da Jonatan, ɗansa, da dukan fādawansa, cewa yana shiri ya kashe Dawuda. Amma Jonatan ɗan Saul yana jin daɗin Dawuda ƙwarai.
2 Jonatan ya faɗa wa Dawuda ya ce, “Saul, mahaifina, yana so ya kashe ka, domin haka sai ka lura da kanka da safe, ka ɓuya a wani lungu.
3 Ni kuwa zan tafi in tsaya kusa da mahaifina a saura inda ka ɓuya, zan yi masa magana a kanka, abin da ya faru, zan sanar da kai.”
4 Jonatan kuwa ya yabi Dawuda a gaban Saul, ya ce masa, “Kada sarki ya yi wa baransa, Dawuda, laifi, gama shi bai yi maka laifi ba, ayyukansa kuma a gare ka masu kyau ne.
5 Ya yi kasai da ransa har ya kashe Bafilisten, Ubangiji kuwa ya ba Isra'ilawa babbar nasara. Kai ma ka gani, ka kuwa yi murna. Me ya sa za ka ɗauki alhakin Dawuda, wanda bai yi maka laifin kome ba?”
6 Saul kuwa ya saurari maganar Jonatan, ya rantse masa ya ce, “Hakika, ba za a kashe shi ba.”
7 Jonatan kuwa ya kira Dawuda ya faɗa masa dukan abin da Saul ya faɗa. Ya kuma kai Dawuda gaban Saul, ya zauna tare da shi kamar dā.