15 Saul kuma ya sāke aiken manzannin su tafi su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi nan wurina a kan gadonsa don in kashe shi.”
16 Da manzannin suka tafi, sai suka tarar da kan gida a gadon, da matashin kai na gashin awaki wajen kansa.
17 Saul kuwa ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya tsere?”Ta ce wa Saul, “Ya ce mini, idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni.”
18 Dawuda ya gudu, ya tsere zuwa wurin Sama'ila a Rama, ya faɗa masa dukan abin da Saul ya yi masa. Shi da Sama'ila suka tafi suka zauna a Nayot.
19 Aka faɗa wa Saul cewa, “Dawuda yana a Nayot ta Rama.”
20 Sai ya aika da manzanni su tafi su kama Dawuda. Da suka kai, suka iske ƙungiyar annabawa suna annabci, Sama'ila kuwa yana tsaye a gabansu. Ruhun Allah ya sauko a kan manzannin Saul, su kuma suka yi annabci.
21 Aka faɗa wa Saul, sai ya sāke aiken waɗansu, su kuma suka shiga yin annabci. Ya kuma sāke aiken manzanni aji na uku, su kuma suka shiga yin annabci.