3 Saul ya isa garken tumaki a gefen hanya, inda akwai kogo. Sai ya shiga cikin kogon don ya huta. Dawuda da mutanensa kuwa suna zaune a ƙurewar kogon.
4 Mutanen Dawuda suka ce masa, “Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka yi yadda ka ga dama da shi.” Dawuda kuwa ya tashi a hankali, ya yanke shafin rigar Saul.
5 Daga baya zuciyar Dawuda ta kāshe shi domin ya yanke shafin rigar Saul.
6 Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji ya sawwaƙa in yi wa ubangijina irin abu haka, har in miƙa hannuna in kashe keɓaɓɓe na Ubangiji.”
7 Da wannan magana Dawuda ya rinjayi mutanensa, bai yarda musu su fāɗa wa Saul ba.Sai Saul ya fita daga kogon ya kama hanya, ya yi tafiyarsa.
8 Daga baya kuma Dawuda ya fita daga kogon, ya yi kira, ya ce, “Ya ubangijina, sarki.” Da Saul ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna.
9 Ya ce wa Saul, “Me ya sa kake kasa kunne ga maganganun mutanen da suke cewa, ‘Dawuda yana nema ya cuce ka?’