11 Ubangiji ya sawwaƙa in miƙa hannuna in taɓa wanda Ubangiji ya keɓe. Sai dai ka ɗauki mashin da butar ruwan da yake wajen kansa, mu tafi.”
12 Da haka Dawuda ya ɗauki mashi da butar ruwan da yake wajen kan Saul, suka tafi. Ba wanda ya gansu, ba wanda ya sani, ba kuwa wanda ya farka, gama dukansu suna barci, domin Ubangiji ne ya sa barci mai nauyi ya share su.
13 Sa'an nan Dawuda ya haye zuwa wancan gefe, ya tsaya can nesa bisa dutsen, da ɗan nisa tsakaninsu.
14 Sai Dawuda ya kira sojojin sansanin, da kuma Abner ɗan Ner, ya ce, “Ba za ka amsa mini ba, Abner?”Sai Abner ya ce, “Wa yake kiran sarki?”
15 Dawuda ya ce wa Abner, “Kai ba namiji bane? Wa yake kama da kai cikin Isra'ila? Me ya sa ba ka lura da mai girma, sarki ba? Wani mutum ya zo don ya hallaka mai girma sarki.
16 Abin da ka yi ba shi da kyau. Ka isa a kashe ka, da yake ba ka lura da mai girma ba, wanda Ubangiji ya keɓe. Ka duba, ina mashin sarki da butar ruwan da yake wajen kansa suke?”
17 Saul ya gane da muryar Dawuda, ya ce, “Muryarka ke nan ɗana, Dawuda?”Dawuda ya amsa, “I, muryata ce, ya mai girma sarki.”