2 Saul kuwa ya tashi ya tafi jejin Zif tare da zaɓaɓɓu dubu uku (3,000) na Isra'ila don ya nemi Dawuda.
3 Ya kafa sansaninsa a kan tudun Hakila wanda yake gefen hanya, a gaban Yeshimon. Amma Dawuda ya yi zamansa a jeji. Da ya ga Saul ya bi shi cikin jejin,
4 sai ya aiki magewaya, suka tabbata lalle Saul ya zo.
5 Dawuda kuwa ya tashi ya tafi wurin da Saul ya kafa sansani. Ya kuwa ga inda Saul yake kwance, da kuma Abner ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul. Saul ya kwanta a sansanin, sojojin suna kewaye da shi.
6 Dawuda ya ce wa Ahimelek Bahitte, da Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab, “Wa zai tafi tare da ni zuwa sansanin Saul?”Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”
7 Sai Dawuda da Abishai, suka tafi sansanin Saul da dare. Suka tarar da Saul yana barci cikin sansani da mashinsa a kafe a ƙasa, wajen kansa. Abner kuwa da sauran sojoji suna kwance kewaye da shi.
8 Sa'an nan Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka bar ni in nashe shi da mashi sau ɗaya kaɗai, in sha zararsa, in haɗa shi da ƙasa!”