1 A kwanakin nan Filistiyawa suka tattara sojojinsu don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Akish kuwa ya ce wa Dawuda, “Sai ka sani fa, kai da mutanenka za ku tafi tare da ni da sojojina.”
2 Sai Dawuda ya ce, “Za ka ga abin da baranka zai yi.”Akish ya ce wa Dawuda, “Da kyau, zan sa ka cikin zaunannun jarumawan da suke kāre ni.”
3 Sama'ila ya riga ya rasu, dukan Isra'ilawa kuwa suka yi makoki dominsa, suka binne shi a garinsu, wato Rama. Saul kuma ya riga ya kori masu duba da masu maita daga ƙasar.
4 Filistiyawa suka kafa sansaninsu a Shunem. Saul ya tattara Isra'ilawa, su ma suka kafa sansaninsu a Gilbowa.
5 Da Saul ya ga rundunar yaƙin Filistiyawa, sai ya tsorata, ya yi rawar jiki ƙwarai.
6 Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, Ubangiji bai amsa masa ba, ko ta mafarkai, ko ta Urim, ko ta annabawa.
7 Sai ya ce wa barorinsa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.”Barorinsa suka ce masa, “Ai, akwai wata mai duba a Endor.”