1 Akwai wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sunansa Kish, ɗan Abiyel, jikan Zeror, na iyalin Bekorat, dangin Afinya, shi attajiri ne.
2 Yana da wani ɗa, sunansa Saul, kyakkyawan saurayi ne. A cikin jama'ar Isra'ila ba wanda ya fi shi kyau, ya fi kowa tsayi a cikin Isra'ilawa duka.
3 Ana nan sai jakunan Kish, mahaifin Saul suka ɓace, Kish kuwa ya ce wa Saul, ɗansa, “Tashi, kai da ɗaya daga cikin barorin ku tafi, ku nemo jakunan.”
4 Suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, suka ratsa ta ƙasar Shalisha, amma ba su same su ba. Suka kuma bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba. Sai suka bi ta ƙasar Biliyaminu, amma ba su same su ba.
5 Da suka kai ƙasar Zuf, sai Saul ya ce wa baransa da yake tare da shi, “Zo mu koma gida, kada babana ya bar damuwa a kan jakunan ya yi ta damuwa a kanmu.”
6 Amma baran ya ce masa, “Ai, akwai wani mutumin Allah a garin nan, ana kuwa ganin girmansa, domin duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa, watakila ya iya faɗa mana inda jakunanmu suke.”