11 Zadakiya ɗan Kena'ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan ƙahoni za ka tunkuyi Suriyawa har su hallaka.’ ”
12 Dukan annabawan suka yi annabci iri ɗaya, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot, za ka yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
13 Bafāden da ya tafi kiran Mikaiya ya ce masa, “Ga shi, maganar sauran annabawan iri ɗaya ce, sun yi maganar alheri ga sarki, sai kai ma ka yi magana irin tasu, ka yi maganar alheri ga sarki.”
14 Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”
15 Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?”Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
16 Sarki Ahab kuwa ya ce masa, “Sau nawa zan roƙe ka kada ka faɗa mini kome sai dai gaskiya ta Ubangiji?”
17 Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra'ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, ‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.’ ”