20 Tsawon Wuri Mafi Tsarki na can ciki kamu ashirin ne, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu ashirin. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa. Ya kuma yi bagadensa da itacen al'ul.
21 Sulemanu ya dalaye cikin Haikalin da zinariya tsantsa. Ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki, sa'an nan ya dalaye su da zinariya.
22 Ya dalaye dukan cikin Haikalin da zinariya, ya kuma dalaye bagaden da yake Wuri Mafi Tsarki na can ciki, da zinariya.
23 Ya yi kerubobi guda biyu da itacen zaitun, ya sa su cikin Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.
24-25 Dukan kerubobin irinsu ɗaya girmansu kuma ɗaya. Tsawon kowane fiffike na kerub ɗin kamu biyar, wato tsawon daga ƙarshen wannan fiffike zuwa ƙarshen wancan fiffike kamu goma ne.
26 Tsayin kowane kerub kamu goma ne.
27 Ya sa kerubobin daura da juna a can cikin Haikali domin fikafikan su taɓi juna a tsakiya kowane ɗayan kuma ya taɓi bango.