25 Amma sarki ya ce wa Absalom, “A'a ɗana, ba ma tafi duka ba, don kada mu nawaita maka.” Absalom ya dāge cewa, sai sarki ya je, amma duk da haka sarki bai tafi ba, sai dai ya sa masa albarka.
26 Sa'an nan Absalom ya ce, “Idan ba za ka tafi ba, ina roƙonka ka bar Amnon ɗan'uwana ya tafi tare da mu.”Sarki ya ce, “Don me zai tafi tare da kai?”
27 Amma Absalom ya dāge har sarki ya yarda. Amnon da dukan 'ya'yan sarki suka tafi tare da shi.
28 Absalom ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku lura sa'ad da Amnon ya bugu da ruwan inabi, in na ce, ‘Bugi Amnon’, sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro, gama ni na umarce ku, sai dai ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka.”
29 Haka kuwa barorin Absalom suka kashe Amnon yadda Absalom ya umarta. Sauran 'ya'yan sarki kuwa suka tashi, kowa ya hau alfadarinsa, ya gudu.
30 Sa'ad da suke kan hanya labari ya kai kunnen Dawuda. Aka ce, “Absalom ya kashe dukan 'ya'yan sarki, ba wanda ya tsira daga cikinsu.”
31 Sai sarki ya tashi ya keta rigunansa, ya kwanta a ƙasa. Dukan barorinsa kuma da suke tsaye a wurin suka kyakketa rigunansu.