24 Sarki ya ce a sa shi ya koma gidansa, kada ya zo gabansa. Absalom kuwa ya yi zamansa can gidansa, bai je gaban sarki ba.
25 A cikin Isra'ila duka ba wanda ake yaba kyansa kamar Absalom. Tun daga tafin sawunsa har zuwa bisa kansa ba shi da makusa.
26 Sa'ad da ya yi aski yakan auna nauyin gashin kansa, nauyin yakan kai wajen shekel ɗari biyu. Gama a ƙarshen kowace shekara yake aski, sa'ad da gashin ya yi masa nauyi.
27 Aka haifa wa Absalom 'ya'ya uku maza da 'ya mace guda, sunanta Tamar, ita kuwa kyakkyawa ce.
28 Absalom ya yi shekara biyu cif a Urushalima, amma bai sami izinin ganin sarki ba.
29 Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don ya aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Ya kuma sāke aikawa, Yowab kuwa ya ƙi zuwa.
30 Sai ya ce wa barorinsa, “Ga Yowab yana da gonar sha'ir kusa da tawa, ku tafi, ku sa mata wuta.” Barorin Absalom kuwa suka tafi suka sa wa gonar wuta.