1 Wannan waƙa Dawuda ya raira wa Ubangiji sa'ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun Saul da dukan sauran abokan gābansa, ya ce,
2 “Ubangiji ne mai cetona,Shi ne ƙaƙƙarfar kagarata.
3 Allahna, shi ne kāriyata,Ina zaune lafiya tare da shi.Yana kāre ni kamar garkuwa,Yana tsare ni, ya kiyaye ni.Shi ne mai cetona.
4 Na yi kira ga Ubangiji,Ya cece ni daga abokan gābana.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
5 Gama raƙuman ruwa na mutuwa sun kewaye ni,Raƙuman ruwa na hallaka suna gangarawa ta kaina.
6 Mutuwa ta ɗaure ni da igiyoyinta da ƙarfi,Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
7 A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji,Na yi kira ga Allah domin taimako.Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata,Ya kasa kunne ga kukana na neman taimako.