39 Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.
40 “Za su kuta taron mutane a kanki, za su jajjefe ki da duwatsu, su yayanka ki gunduwa gunduwa da takubansu.
41 Za su kuma ƙone gidajenki, su hukunta ki a gaban mata da yawa. Ni kuwa zan sa ki bar karuwanci, ba za ki ƙara ba da kuɗi ga kwartayenki ba.
42 Sa'an nan fushina a kanki zai huce, kishina a kanki zai ƙare. Zan huce, ba zan yi fushi ba kuma.
43 Da yake ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, domin haka zan sāka miki alhakin ayyukanki. Kin yi lalata, banda ayyukanki na banƙyama kuma, ni Ubangiji na faɗa.”
44 Ubangiji ya ce, “Ga shi, duk mai yin amfani da karin magana, zai faɗi wannan karin magana a kanki. ‘Kamar yadda mahaifiya take haka 'yar take.’
45 Ke 'yar mahaifiyarki ce wadda ta ƙi mijinta da 'ya'yanta. Ke kuma 'yar'uwar 'yar'uwanki mata ce waɗanda suka ƙi mazansu da 'ya'yansu. Mahaifiyarki Bahittiya ce, mahaifinki kuwa Ba'amore ne.