22 Zan ceci garken tumakina, ba za su ƙara zama ganima ba. Zan kuma shara'anta tsakanin tunkiya da tunkiya.
23 Zan sa musu makiyayi guda, wato bawana Dawuda. Zai yi kiwonsu, ya zama makiyayinsu.
24 Ni kuma, Ubangiji, zan zama Allahnsu. Bawana Dawuda kuwa zai zama sarkinsu.’ Ni Ubangiji na faɗa.
25 “Zan yi alkawarin salama da su. Zan kuwa kori namomin jeji daga ƙasar, domin tumakin su zauna lafiya a jeji, su kwana cikin kurmi.
26 Zan sa su, da wuraren da suke kewaye da tuduna dalilin samun albarka. Zan aiko da ruwan sama a lokacinsa, zai kuma zama ruwan albarka.
27 Itatuwan saura za su yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani. Za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.
28 Ba za su ƙara zama ganimar al'ummai ba, namomin jejin ƙasar kuma ba za su cinye su ba. Za su yi zamansu lafiya, ba wanda zai tsorata su.