38 Akwai ɗaki, wanda ƙofarsa take duban ginshiƙan gyaffan ƙofofin, a wurin ake wanke hadayar ƙonawa.
39 A shirayin ƙofar akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yanka hadayar ƙonawa, da hadaya don zunubi da laifi.
40 Akwai tebur biyu a sashin waje na shirayin ƙofar arewa, akwai kuma waɗansu tebur biyu a ɗayan sashin shirayin ƙofar.
41 A gab da ƙofar akwai tebur huɗu, a waje ɗaya kuma akwai huɗu. Duka guda takwas ke nan, inda za a riƙa yanka dabbobin da za a yi hadaya da su.
42 Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu, tsawon da faɗin kowanne kamu ɗaya da rabi rabi ne, tsayi kuwa kamu guda ne. A nan za a ajiye kayan yanka hadayar ƙonawa, da ta sadaka.
43 Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye da cikin ɗakin, tsawonsu taƙi-taƙi. Za a riƙa ajiye naman hadaya a kan teburorin.
44 Ya kai ni fili na can ciki, sai ga ɗakuna biyu a filin. Ɗaya yana wajen ƙofar arewa, yana fuskantar kudu. Ɗayan kuma yana wajen ƙofar kudu yana fuskantar arewa.