12 Zai zama rabonsu daga tsattsarkan yankin ƙasar da take kusa da yankin Lawiyawa.
13 Gab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗi kuma kamu dubu goma [10,000]. Tsawonsa duka zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗi kuwa kamu dubu goma [10,000].
14 Daga cikinsa ba za su sayar ba, ko su musayar, ba kuma za su jinginar da wannan keɓaɓɓen yankin ƙasa ba, gama tsattsarka ne na Ubangiji.
15 “Ragowar yankin mai faɗin kamu dubu biyar [5,000], da tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], zai zama hurumin birnin, inda za a yi gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar yankin.
16 Ga yadda girman birnin zai kasance, a wajen arewa kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen kudu kuwa kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen gabas kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen yamma kuma kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500].
17 Birnin zai kasance da hurumi a kewaye da shi. A wajen gabas kamu metan da hamsin, a wajen yamma kamu metan da hamsin, a wajen kudu kamu metan da hamsin, a wajen arewa kuma kamu metan da hamsin.
18 Ragowar tsawon yankin da yake gab da tsattsarkan yankin, zai zama kamu dubu goma [10,000] a wajen gabas, a wajen yamma kamu dubu goma [10,000]. Amfanin da yankin zai bayar, zai zama abincin ma'aikatan birnin.