22 Ko da za ka yi wanka da sabulunsalo,Ka yi amfani da sabulu mai yawa,Duk da haka zan ga tabbanzunubanka.Ni Ubangiji Allah na faɗa.
23 Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar dakanka ba,Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba?Ka duba hanyarka ta zuwa cikinkwari, ka san abin da ka yi.Kana kama da taguwa, mai yawonneman barbara.
24 Kamar jakar jeji kake, wadda takeson barbara,Wadda take busar iska,Sa'ad da take son barbara, wa zai iyahana ta?Jakin da take sonta, ba ya bukatarwahalar da kansaGama a watan barbararta za a sameta.
25 Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunkaba takalma,Kada kuma ka bar maƙogwaronkaya bushe.Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani,Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwazan bi.’
26 “Kamar yadda ɓarawo yakan shakunya sa'ad da aka kama shi,Haka nan mutanen Isra'ila za su shakunya,Da su, da sarakunansu, dashugabanninsu,Da firistocinsu, da annabawansu.
27 Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai nemahaifinmu.’Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, kahaife mu.’Gama sun ba ni baya, ba su fuskanceni ba.Amma sa'ad da suke shan wahala,sukan ce,‘Ka zo ka taimake mu.’
28 Ina gumakan da kuka yi wakanku?Bari su tashi in sun iya cetonkulokacin wahalarku.Yahuza, yawan gumakanku sun kaiYawan garuruwanku.