1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya sa'ad da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da dukan sojojinsa, da dukan sojojin mulkokin al'umman da suke a ƙarƙashinsa, da dukan mutane suke yaƙi da Urushalima da dukan biranenta.
2 Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce wa Irmiya ya tafi, ya faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza cewa, “Ni Ubangiji, zan ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa ƙone shi da wuta.
3 Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila.
4 Ya Zadakiya, Sarkin Yahuza, ka ji maganar da ni Ubangiji na faɗa a kanka, ba za ka mutu ta wurin takobi ba.