19 Zan komar da Isra'ila a makiyayarsa, zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Zai sami biyan bukatarsa a tsaunukan Ifraimu da na Gileyad.
20 Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.
21 “Ku haura ku fāɗa wa ƙasarMeratayim da mazaunan Fekod.Ku kashe, ku hallaka su sarai,Ku aikata dukan abin da na umarceku,Ni Ubangiji na faɗa.
22 Hargowar yaƙi tana cikin ƙasar,Da kuma babbar hallakarwa!
23 Ga yadda aka karya gudumar dukanduniya!Ga yadda Babila ta zama abarƙyama ga sauran al'umma!
24 Na kafa miki tarko, ya kuwa kamaki, ya Babila,Ke kuwa ba ki sani ba.An same ki, an kama,Domin kin yi gāba da ni.”
25 Ubangiji ya buɗe taskarmakamansa,Ya fito da makaman hasalarsa,Gama Ubangiji Allah Mai Rundunayana da aikin da zai yi a ƙasarKaldiyawa.