5 Za su tambayi hanyar Sihiyona, sa'an nan su bi ta, suna cewa, ‘Bari mu haɗa kanmu don mu yi madawwamin alkawari da Ubangiji, alkawari wanda ba za a manta da shi ba.’
6 “Mutanena sun zama kamar ɓatattuntumaki,Waɗanda makiyayansu suka bauɗarda su,Suka ɓata a cikin tsaunuka,Suna kai da kawowa daga wannandutse zuwa wancan.Sun manta da shingensu.
7 Duk waɗanda suka same su, suncinye su.Maƙiyansu suka ce, ‘Ba mu yi laifiba,’Gama sun yi wa Ubangiji laifi,wanda yake tushen gaskiya,Ubangiji wanda kakanninsu sukadogara gare shi.
8 “Ku gudu daga cikin Babila,Ku fita kuma daga cikin ƙasarKaldiyawa,Ku zama kamar bunsurai waɗandasuke ja gaban garke.
9 Ga shi, zan kuta manyan ƙasashedaga arewaSu faɗa wa Babila da yaƙi.Za su ja dāgar yaƙi gāba da ita, sucinye ta.Kibansu kamar na gwanayenmayaƙa neWaɗanda ba su komowa banza.
10 Za a washe Kaldiyawa,Waɗanda suka washe su kuwa za suƙoshi,Ni Ubangiji na faɗa.
11 “Saboda kuna murna, kuna farinciki,Ku da kuka washe gādona,Saboda kuma kuna tsalle kamarkarsana a cikin ciyawa,Kuna haniniya kamar ingarmu,