1 Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, 'yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna.
2 Sarki Zadakiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehoyakim ya yi.
3 Al'amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra'ila da Yahuza, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala.Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.
4 A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina garu kewaye da ita.
5 An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zadakiya.
6 A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.
7 Sai aka huda garun birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa'ad da Kaldiyawan take kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.