12 Sauran da suka ragu za su fi zinariya wuyar samuwa.
13 Zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuwa za a girgiza ta a inda take, a wannan rana sa'ad da ni, Ubangiji Mai Runduna, na nuna fushina.
14 “Baƙin da yake zaune a Babila za su gudu zuwa ƙasashensu, suna a warwatse kamar bareyin da suke tsere wa maharbansu, kamar tumakin da ba su da makiyayi.
15 Duk wanda aka kama za a soke shi ya mutu.
16 Sa'ad da suke cikin halin ƙaƙa naka yi, za a fyaɗa 'ya'yansu ƙasa, su mutu. Za a washe gidajensu, a yi wa matansu faɗe.”
17 Ubangiji ya ce “Ina zuga mutanen Mediya, don su faɗa wa Babila da yaƙi. Ba su kula da azurfa ba, ba kuwa za a jarabce su da zinariya ba.
18 Da bakkuna da kibansu, za su karkashe samari. Ba za su nuna jinƙai ga jarirai ba, ba kuwa za su ji tausayin 'yan yara ba.