17 Sai Isra'ilawa suka raira waƙa, suka ce,“Rijiya, ki ɓuɓɓugo da ruwaMu kuwa za mu raira waƙa mu gaishe ta!
18 Rijiyar da hakimai suka haƙa,Shugabannin jama'a suka haƙa,Da sandan sarauta,Da kuma sandunansu.”Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana.
19 Daga Mattana suka tafi Nahaliyel suka tafi Bamot.
20 Daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake a ƙasar Mowab wajen ƙwanƙolin Dutsen Fisga wanda yake fuskantar hamada.
21 Mutanen suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon, Sarkin Amoriyawa, suka ce masa,
22 “Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka, ba za mu ratsa ta cikin gonaki, ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai, har mu fita daga karkararka.”
23 Amma Sihon bai yarda wa Isra'ilawa su ratsa ta karkararsa ba. Sai ya tattara mazajensa, suka fita don su yi yaƙi da Isra'ilawa a jejin. Suka tafi Yahaza suka yi yaƙi da Isra'ilawa.