18 Rijiyar da hakimai suka haƙa,Shugabannin jama'a suka haƙa,Da sandan sarauta,Da kuma sandunansu.”Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana.
19 Daga Mattana suka tafi Nahaliyel suka tafi Bamot.
20 Daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake a ƙasar Mowab wajen ƙwanƙolin Dutsen Fisga wanda yake fuskantar hamada.
21 Mutanen suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon, Sarkin Amoriyawa, suka ce masa,
22 “Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka, ba za mu ratsa ta cikin gonaki, ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai, har mu fita daga karkararka.”
23 Amma Sihon bai yarda wa Isra'ilawa su ratsa ta karkararsa ba. Sai ya tattara mazajensa, suka fita don su yi yaƙi da Isra'ilawa a jejin. Suka tafi Yahaza suka yi yaƙi da Isra'ilawa.
24 Isra'ilawa kuwa suka karkashe su da takobi, suka mallaki ƙasarsa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa kan iyakar Ammonawa, gama Yahaza ita ce kan iyakar Ammonawa.