17 Yanzu dai rani ne, ko ba haka ba? Zan roƙi Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama, da haka za ku sani, ku kuma ga babbar muguntar da kuka yi wa Ubangiji da kuka roƙa a yi muku sarki.”
18 Sai Sama'ila ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa aka yi tsawa da ruwan sama a wannan rana. Dukan jama'a kuwa suka ji tsoron Ubangiji da Sama'ila ƙwarai.
19 Suka ce wa Sama'ila, “Ka yi wa bayinka roƙo ga Ubangiji Allahnka don kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”
20 Sama'ila kuwa ya ce musu, “Kada ku razana, gama kun riga kun aikata wannan mugunta, duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta masa da zuciya ɗaya.
21 Kada kuma ku ratse ku bi abubuwa marasa amfani da ba za su amfane ku, ko su cece ku ba, gama ba su da wani amfani.
22 Gama Ubangiji ya yi ƙaƙƙarfan alkawari, ba zai yashe ku ba, gama ya ɗauri aniya ya maishe ku jama'arsa.
23 Amma ni kaina, Allah ya sawwaƙa in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin fasa yin addu'a ga Ubangiji dominku. Zan riƙa koya muku kyawawan abubuwan da suke daidai.