4 Jama'a suka amsa, suka ce, “Ba ka zalunci kowa ba, ba ka wulakanta kowa ba, ba ka kuma yi wa kowa ƙwace ba.”
5 Sa'an nan ya ce musu, “Ubangiji shi ne shaida, wanda kuma ya naɗa, shi ma shaida ne a yau, cewa ba ku iske ni da laifin kome ba.”Jama'ar suka ce, “Ubangiji ne shaida.”
6 Sama'ila kuma ya ce wa jama'a, “Ubangiji ne ya sa Musa da Haruna su fito da kakanninku daga ƙasar Masar.
7 Yanzu fa ku tsaya shiru don in yi muku magana a kan ayyuka masu adalci na Ubangiji waɗanda ya aikata dominku da kakanninku.
8 Sa'ad da Yakubu da 'ya'yansa suka tafi Masar, Masarawa suka wulakanta su, sai suka kai kuka ga Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiki Musa da Haruna waɗanda suka fito da kakanninku daga ƙasar Masar, suka kawo su su zauna a wannan wuri.
9 Amma suka bar bin Ubangiji Allahnsu. Ubangiji kuwa ya bashe su a hannun Sisera, shugaban rundunar Yabin, Sarkin Hazor, da a hannun Filistiyawa, da kuma a hannun Sarkin Mowab, suka yāƙe su.
10 Sai suka yi wa Ubangiji kuka, suka ce, ‘Mun yi laifi domin mun bar bin Ubangiji, muka bauta wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot, amma yanzu muna roƙonka ka cece mu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.