9 Amma suka bar bin Ubangiji Allahnsu. Ubangiji kuwa ya bashe su a hannun Sisera, shugaban rundunar Yabin, Sarkin Hazor, da a hannun Filistiyawa, da kuma a hannun Sarkin Mowab, suka yāƙe su.
10 Sai suka yi wa Ubangiji kuka, suka ce, ‘Mun yi laifi domin mun bar bin Ubangiji, muka bauta wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot, amma yanzu muna roƙonka ka cece mu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.
11 Ubangiji kuwa ya aika musu da Yerubba'al, wato Gidiyon, da Barak, da Yefta, da Samson, suka cece ku daga hannun abokan gābanku ta kowace fuska. Sa'an nan kuka yi zamanku lafiya.
12 Amma da kuka ga Nahash Sarkin Ammonawa ya zo don ya yi yaƙi da ku, sai kuka ce mini, ‘Mu dai a yi mana sarki da zai sarauce mu,’ alhali kuwa Ubangiji Allahnku ne Sarkinku.
13 To, ga sarkin da kuka zaɓa nan, kuka roƙa. Ga shi, Ubangiji ya naɗa muku shi.
14 Idan za ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa, ku yi biyayya da maganarsa, ba za ku karya umarnin Ubangiji ba, idan kuma ku da sarkin da yake sarautarku za ku bi Ubangiji Allahnku, kome zai zamar muku daidai.
15 Amma idan kun ƙi yin biyayya da maganar Ubangiji, kuka kuma karya umarnin Ubangiji, to, Ubangiji zai yi gāba da ku da sarkinku.