12 Da haka za mu tafi mu neme shi duk inda yake, mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo bisa ƙasa. Da shi da mutanensa, ba wanda za a bari da rai.
13 Idan ya gudu zuwa cikin gari, sai dukan jama'armu su zarge garin da igiya, su jā har duk ya watse, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”
14 Sai Absalom da dukan mutanen Isra'ila suka ce, “Shawarar Hushai Ba'arkite ta fi ta Ahitofel kyau.” Haka Ubangiji ya nufa ya wofintar da kyakkyawar shawarar Ahitofel don ya jawo wa Absalom masifa.
15 Sa'an nan Hushai ya ce wa Zadok da Abiyata, firistoci, “Ga irin shawarar da Ahitofel ya ba Absalom da dattawan Isra'ila, ga kuma irin wadda ni na bayar.
16 Yanzu sai ka aika da sauri a faɗa wa Dawuda, kada ya kwana a bakin jeji a daren yau, amma ya haye don kada a hallaka shi tare da mutanensa.”
17 Jonatan da Ahimawaz suna jira a En-rogel. Wata baranya takan tafi ta faɗa musu saƙo, su kuma sai su tafi su faɗa wa sarki Dawuda, don kada a gan su suna shiga birnin.
18 Amma wani saurayi ya gan su, sai ya faɗa wa Absalom. Sai su biyu ɗin suka gudu nan da nan. Suka shiga gidan wani mutum a Bahurim, akwai rijiya a filin gidan. Sai suka shiga rijiyar.