9 “Ya maigirma sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu da suka saka annabi Irmiya cikin fijiya, Zai mutu can da yunwa, gama ba sauran abinci a birnin.”
10 Sa'an nan sarki ya umarci Ebedmelek, mutumin Habasha, ya tafi da mutum talatin su tsamo annabi Irmiya daga cikin rijiyar kafin ya mutu.
11 Sai Ebed-melek ya tafi da mutanen, ya kuma tafi gidan sarki, a ɗakin ajiya, ya kwaso tsummoki da tsofaffin tufafi, ya zurara wa Irmiya a rijiyar.
12 Ebedmelek, mutumin Habasha, ya ce wa Irmiya ya sa tsummokin da tsofaffin tufafin a hammatarsa, ya zarga igiya, Irmiya kuwa ya yi yadda aka ce masa.
13 Suka jawo Irmiya da igiyoyi, suka fito da shi daga rijiya. Irmiya kuwa ya zauna a gidan waƙafi.
14 Sarki Zadakiya ya aika a kirawo annabi Irmiya. Ya tafi ya sadu da Irmiya a ƙofa ta uku ta Haikalin Ubangiji. Sarki kuwa ya ce wa Irmiya, “Zan yi maka tambaya, kada kuwa ka ɓoye mini kome.”
15 Irmiya kuwa ya ce wa Zadakiya, “Idan na faɗa maka gaskiya za ka kashe ni, idan kuma na ba ka shawara, ba za ka karɓi shawarata ba.”