4 Sai na ce,“Waɗannan mutane ba su da kirki,Ba su da hankali,Ba su san hanyar Ubangiji,Ko shari'ar Allahnsu ba.
5 Zan tafi wurin manyan mutane, in yimusu magana,Gama sun san nufin Ubangiji, dashari'ar Allahnsu.”Amma dukansu sun ƙi yardaUbangiji ya mallake su,Suka ƙi yi masa biyayya.
6 Domin haka zaki daga kurmi zaikashe su,Kyarkeci kuma daga hamada zaihallaka su.Damisa tana yi wa biranensukwanto,Duk wanda ya fita daga cikinsu sai ayayyage shi,Domin laifofinsu sun yi yawa,Karkacewarsu babba ce.
7 “Don me zan gafarce ki?'Ya'yanki sun rabu da ni,Sun yi rantsuwa da gumaka,Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai,Suka yi karuwanci, suka ɗungumazuwa gidajen karuwai,
8 Kamar ƙosassun ingarmu suke,masu jaraba,Kowa yana haniniya, yana nemanmatar maƙwabcinsa.
9 Ba zan hore su saboda waɗannanabubuwa ba?Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wakaina fansa a kan wannanal'umma ba?
10 Ku haura, ku lalatar da gonarkurangar inabinta,Amma kada ku yi mata ƙarƙaf,Ku sassare rassanta,Gama su ba na Ubangiji ba ne.