8 “Al'ummai masu yawa za su wuce ta gefen wannan birni, kowane mutum zai ce wa maƙwabcinsa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’
9 Za su amsa, su ce, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada ga gumaka, suka bauta musu.’ ”
10 Ku mutanen Yahuza, kada ku yikuka saboda sarki Yosiya,Kada ku yi makokin rasuwarsa,Amma ku yi kuka ƙwarai sabodaɗansa Yehowahaz.Sun ɗauke shi, sun tafi da shi, ba zaiƙara komowa ba,Ba kuma zai ƙara ganin ƙasar daaka haife shi ba.
11 Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.
12 Amma a wurin da suka kai shi zaman talala, a can zai mutu, ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.
13 Kaiton wanda ya gina gidansa tahanyar rashin adalci,Benayensa kuma ta hanyar rashingaskiya.Wanda ya sa maƙwabcinsa ya yimasa aiki a banza,Bai ba shi hakkinsa ba.
14 Kaiton wanda ya ce,“Zan gina wa kaina babban gidaDa waɗansu irin benayemusamman.”Ya yi masa tagogi,Ya manna masa itacen al'ul,Sa'an nan ya yi masa jan shafe.