1 Albarka ta tabbata ga mutumin daBa ya karɓar shawarar mugaye,Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi,Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.
2 Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari'ar Allah,Yana ta nazarinta dare da rana.
3 Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama,Yakan ba da 'ya'ya a kan kari,Ganyayensa ba sa yin yaushi,Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.
4 Amma mugaye ba haka suke ba,Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.
5 Allah kuwa zai hukunta mugaye,Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.
6 Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai,Amma al'amuran mugaye za su watse.