1 Ka yi mana jinƙai, ya Allah, ka sa mana albarka,Ka dube mu da idon rahama,
2 Domin dukan duniya ta san nufinka,Dukan sauran al'umma kuma su san cetonka.
3 Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah,Da ma dukan mutane su yabe ka!
4 Da ma sauran al'umma su yi murna, su raira waƙa ta farin ciki,Domin kana yi wa jama'a shari'a ta adalci,Kana kuma bi da dukan sauran al'umma.
5 Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah,Da ma dukan mutane su yabe ka!
6 Ƙasa ta ba da amfaninta,Allah, wanda yake Allahnmu ne, ya sa mana albarka.
7 Allah ya sa mana albarka,Da ma dukan jama'a ko'ina su girmama shi.