1 Ya Ubangiji, ina zuba ido gare ka,A Sama inda kake mulki.
2 Kamar yadda bara yake dogara ga maigidansa,Baranya kuma ga uwargijiyarta,Haka nan muke zuba ido gare ka, ya Ubangiji Allahnmu,Har mu sami jinƙanka.
3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,An gwada mana wulakanci matuƙa!
4 Attajirai sun daɗe suna ta yi mana ba'a,Azzalumai masu girmankai sun raina mu!