1 Ku yabi Ubangiji, ku alloli,Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa.
2 Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,Ku rusuna a gaban Mai Tsarki sa'ad da ya bayyana.
3 An ji muryar Ubangiji a kan tekuna,Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.
4 An ji muryar UbangijiA dukan ikonsa da zatinsa!
5 Muryar Ubangiji takan karya itatuwan al'ul,Har ma da itatuwan al'ul na Lebanon.
6 Yakan sa duwatsun Lebanon su yi tsalle kamar 'yan maruƙa,Ya kuma sa Dutsen Harmon ya yi tsalle kamar ɗan maraƙi.
7 Muryar Ubangiji ta sa walƙiya ta walƙata.
8 Muryarsa ta sa hamada ta girgiza,Ta girgiza hamadar Kadesh.
9 Muryar Ubangiji ta sa barewa ta haihu,Ta sa itatuwa su kakkaɓe,Sa'ad da aka yi sowa a cikin Haikalinsa,Aka ce, “Daukaka ga Allah!”
10 Ubangiji yana sarautar ruwa mai zurfi,Yana sarauta kamar sarki har abada.
11 Ubangiji yana ba jama'arsa ƙarfi,Ya sa musu albarka da salama.