1 Ina kira ga Ubangiji don neman taimako,Ina roƙonsa.
2 Na kawo masa dukan koke-kokena,Na faɗa masa dukan wahalaina.
3 Sa'ad da na yi niyyar fid da zuciya,Ya san abin da zan yi.A kan hanyar da zan biMaƙiyana sun kafa mini tarko a ɓoye.
4 Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni,Ba wanda zai kiyaye ni,Ba kuwa wanda ya kula da ni.
5 Ya Ubangiji, na kawo kuka gare ka na neman taimako,Ya Ubangiji, kai ne mai kiyaye ni,Kai kaɗai nake so a rayuwata duka.
6 Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako,Gama na nutsa cikin fid da zuciya.Ka cece ni daga maƙiyanaWaɗanda suka fi ƙarfina.
7 Ka cece ni daga cikin wahalata,Sa'an nan zan yabe ka cikin taron jama'arka,Domin ka yi mini alheri.