Zab 37 HAU

Makomar Mugaye da ta Nagargaru

1 Kada ka damu saboda mugaye,Kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.

2 Za su shuɗe kamar busasshiyar ciyawa,Za su mutu kamar yadda tsire-tsire suke bushewa.

3 Ka dogara ga Ubangiji ka aikata nagarta,Ka zauna a ƙasar, ka sami lafiya.

4 Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji,Zai kuwa biya maka bukatarka.

5 Ka miƙa kanka ga Ubangiji,Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.

6 Zai sa nagartarka ta haskaka kamar haske,Adalcinka kuma yă haskaka kamar tsakar rana.

7 Ka natsu a gaban Ubangiji,Ka yi haƙuri, ka jira shi,Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya,Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.

8 Kada ka yi fushi, kada ka hasala!Kada ka damu! Gama ba zai yi maka amfanin kome ba.

9 Waɗanda suka dogara ga Ubangiji,Za su yi zamansu lafiya a ƙasar,Amma za a kori mugaye.

10 A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe,Za ka neme su, amma ba za a same su ba,

11 Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar,Su ji daɗin cikakkiyar salama.

12 Mugu yakan yi wa mutumin kirki makarƙashiya,Yana harararsa da ƙiyayya.

13 Ubangiji yana yi wa mugu dariya,Domin Ubangiji ya sani ba da daɗewa ba mugun zai hallaka.

14 Mugaye sun zare takuba,Sun tanƙware bakkunansuDon su kashe matalauta da masu bukata,Su karkashe mutanen kirki.

15 Amma takubansu za su sassoke su,Za a kakkarya bakkunansu.

16 Ƙanƙanen abin da mutumin kirki yake da shi,Ya fi dukan dukiyar mugaye amfani,

17 Gama Ubangiji zai raba mugaye da ƙarfinsu,Amma zai kiyaye mutanen kirki.

18 Ubangiji yana kula da masu yi masa biyayya,Ƙasar kuwa za ta zama tasu har abada.

19 Ba za su sha wahala a lokacin tsanani ba,Za su sami yalwa a lokacin yunwa.

20 Amma mugaye za su mutu,Magabtan Ubangiji kuwa za su shuɗe kamar furen jeji,Za su ɓace kamar hayaƙi.

21 Mugu yakan ci bashi, yă ƙi biya,Amma mutumin kirki mai alheri ne,Mai bayarwa hannu sake.

22 Waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka,Za su zauna lafiya lau a ƙasar,Amma waɗanda ya la'antaZa a kore su su fita.

23 Ubangiji yakan bi da mutum lafiyaA hanyar da ya kamata yă bi,Yakan ji daɗin halinsa,

24 In ya fāɗi, ba zai yi warwar ba,Gama Ubangiji zai taimake shiYă tashi tsaye.

25 Yanzu dai na tsufa, ni ba yaro ba ne,Amma ban taɓa ganin Ubangiji ya yar da mutumin kirki ba,Ko kuma a ga 'ya'yansa suna barar abinci.

26 A koyaushe yakan bayar a sake,Yana ba da rance ga waɗansu,'Ya'yansa kuwa dalilin albarka ne.

27 Ka rabu da mugunta ka aikata nagarta,Za ka kuwa zauna a ƙasar har abada,

28 Gama Ubangiji yana ƙaunar abin da yake daidai,Ba ya rabuwa da amintattun jama'arsa,Yana kiyaye su koyaushe,Amma za a kori zuriyar mugaye.

29 Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar,Su gāje ta har abada.

30 Kalmomin mutumin kirki suna da hikima,Yana faɗar abin da yake daidai.

31 Yakan riƙe dokar Allahnsa a zuciyarsa, Ba ya kauce mata, faufau.

32 Mugu yakan yi fakon mutumin kirki,Yă yi ƙoƙari yă kashe shi,

33 Amma Ubangiji ba zai bar shi a hannun magabtansa ba,Ko kuwa yă bari a kāshe shiSa'ad da ake masa shari'a.

34 Ka sa zuciyarka ga UbangijiKa kiyaye dokokinsa,Shi zai ba ka ƙarfin da za ka mallaki ƙasar,Za ka kuwa ga an kori mugaye.

35 Na ga wani mugu, azzalumi,Ya fi kowa tsayi,Kamar itacen al'ul na Lebanon,

36 Amma bayan ƙanƙanen lokaci,Da na zaga, ban gan shi ba,Na neme shi, amma ban same shi ba.

37 Dubi mutumin kirki, ka lura da adali,Mutumin salama yakan sami zuriya,

38 Amma za a hallaka masu zunubi ƙaƙaf,Za a kuma shafe zuriyarsu.

39 Ubangiji yakan ceci adalai,Ya kiyaye su a lokatan wahala.

40 Yakan taimake su, yă kuɓutar da su,Yakan cece su daga mugaye,Gama sukan zo wurinsa don yă kāre su.